Labarai

HANGEN TSOHON SHUGABAN KASAR NIGERIA IBB AZABEN 2023.

ZABEN 2023: Na Hango Wani Matashi Da Shekarunsa Basu Wuce 60 Ba Ya Dare Kujerar Shugaban Kasar Najeriya ~ Inji IBB

Tsohon shugaban ƙasar Najeriya na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayyana cewar tuni ya hango wanda zai gaji buzun kujerar shugaba Buhari a kakar zaɓe ta 2023.

IBB ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da akayi da shi a gidan TV na Arise TV.

“Naga wani matashi da shekarunsa basu wuce 60 ba ya ɗare kujerar shugaban ƙasar Najeriya a 2023, kuma wannan matashi ya haɗa duk wata cancanta da nagarta da Najeriya ke buƙata idan har aka bashi damar tsayawa.” Inji IBB

“Ina shawartar ƴan Najeriya da kada su sake su zaɓi mutumin da ya haura shekaru 60 a matsayin shugaban ƙasa.”

“Halin da Najeriya take ciki a yanzu tana buƙatar jagorancin matashi mai ƙwarewa a fannin tattalin arziki da iya siyasa, wanda yake da abokai a dukkan sassan ƙasar nan, wanda ya iya tafiyar da al’umma.” Inji shi

Shin ko wa kuke hasashen tsohon shugaban ƙasa IBB na magana a kansa?

arewanahiya

Farin cikinmu shine ganin farin ciki saman fuskarku muna alfahari duku masoya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button