AN KAMA SOJA DA LAIFIN CIN AMANAR TSARON NIGERIA.
Ankama irin bata garin nan masu lakabin sunan su dana hukuma domin cin zarafin bayin allah cikin ikon Allah yana bada Nasarar kama wadan da dubun su ta cika suke irin wan nan har kar allah ya kara tona asirin su.
Wannan Sojan da kuke gani sunansa Sgt. Thaddeus, yana da lambar aiki da rundinar sojin Nigeria kamar haka 04NA/55/0931
Soja ne wanda yake aiki bangaren sojoji masu lura da abubuwan fashewa “Explosive Ordinance Detector (EOD)
An bashi hutun aiki zai taho garinsa a Kaduna, sai Sojoji suka kamashi a babbar kofar shiga da fita na barikin Sojoji Maimalari Main-gate dake birnin Maiduguri.
Bayan sallamar sa da,akayi domin tafiya hutu ashe yana haka ne domin kaiwa yan ta adda Tallafin Kayan hana kasa zaman lafiya.
An kamashi yana dauke da harsashin bindiga kirar AK47 guda dari da gomasha biyu (112), kuma an kamashi da sinadarin hodar da ake hada bomb (IED)
Binciken farko ya nuna Sajen Thaddeus yana daga daga cikin sojoji manyan maciya amanar tsaron Nigeria wanda suke kaiwa Boko Haram kayan aiki da kuma bandits
Yanzu haka yana hannun military police domin fadada bincike mai tsanani a kansa.
San nan kuma ya bayyana wasu wadan da ya sani da suke irin wan nan aika aika tare na cin zafin mutane domin zalunci.
Muna rokon Allah Ya cigaba da tona asirin maciya amanar tsaron Nigeria a duk inda suke
Datti Assalafy