FARIN CIKIN YAN NIGERIA.
Majalisar Dattawa da ‘yan majalisar wakilan Nigeria sun amince a bawa kananan hukumomin Nigeria ‘yancin cin gashin kansu daga Gwamnonin jihohin Nigeria
Majalisa ta amince kamar yadda Gwamna yake da ‘yancin a zabeshi yayi shekara 4 ko 8 idan ya zarce yana mulki to haka aka bawa shugabannin kananan hukumomi wannan ‘yancin, sai kuma ‘yancin mallakar kudin karamar hukuma
‘Yan majalisun tarayyar Nigeria 258 suka amince da a bawa kananan hukumomi ‘yanci, yayin da ‘yan majalisu 15 ne kacal suka ki amincewa
A bangaren Majalisar Dattawa, Sanatoci 92 ne suka amince a bawa kananan hukumomi ‘yanci, Sanatoci 2 ne kacal suka ki amincewa
Majalisa tayi doka kowace karamar hukuma a Nigeria za’a bude mata account number wanda za’a dinga tura kudin kananan hukumomi kai tsaye daga Gwamnatin tarayya, wato an datsewa Gwamnoni ikon mallakar kudin kananan hukumomi ta kowace hanya
Wallahi wannan matakin da Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta dauka ba karamin tasiri da amfani zai yiwa talakawa ba, yanzu ne talakawan Nigeria zasu fara cin moriyar tsarin mulkin Demokaradiyyah
Shugaba Buhari da duk wanda yake da hannu wajen bawa kananan hukumomi ‘yanci Allah Ya saka musu da alheri