JAMA,AR BIRNIN GWARI NA BIYAN MILIYOYIN KUDI GA YAN BINDIGA SUNA MIKA KU KANSU DAN BUKATAR DAUKI.
Mazauna yankin sun kuma ce hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna ta zama tamkar tarkon mutuwa don bin ta kawai ake yi saboda babu tabbas a kowane lokaci
Bayanai daga ƙaramar hukumar Birnin Gwari, mai fama da hare-haren ‘ya fashin daji sun ce a baya-bayan nan wasu ƙauyuka a yankin sun biya kimanin naira miliyan 45, a matsayin sulhu da ‘yan fashin daji.
Ƙauyukan su fiye da goma a mazaɓar Magajin Gari ta 2 sun biya kuɗaɗen ne bayan ‘yan fashin dajin da ke yankin, suka nemi lallai su biya wannan fansa, matuƙar suna son zaman lafiya.
Birnin Gwari a Kaduna, na cikin yankunan da suka fi fama da taɓarɓarewar tsaro a arewa maso yammacin Najeriya.
Bayanai sun ce wani hari da ‘yan fashin daji suka kai ƙauyen Awaro kimanin mako uku a baya ne, ya ƙara tsorata mutanen yankin har suka miƙa wuya.