Labarai
DALIBAN JAMI,OIN NIGERIA SUNCE SAM BAZA SU LAMINCI KARIN KUDIN MAKARANTA BA.

Majalisar dattawan Najeriya ta shiga tsakanin kungiyar daliban arewacin kasar da kuma hukumomin jami’o’in yankin game da maganar karin kudin makaranta.
‘Ya’yan kungiyar daliban arewacin Najeriyar sun yi barazanar gudanar da zanga-zanga game da karin kudin karatu a makarantun yankin.
Kungiyar daliban ta ce batun karin kudin makaranta a wannan yanayi da ake ciki zai kasance wata babbar matsala ga daliban da ma iyayensu.
Jamilu Aliyu Chiranci, shi ne shugaban gamayyar daliban arewacin Najeriya, ya ce bai kamata a kara kudin makaranta a wannan yanayi da ake ciki a Najeriya na matsin tattalin arziki da rashin aikin yi ga kuma rashin tsaro ba.