YADDA TARON AMRUKAR DA RASHA YA KASANCE.

n yi faɗa kaca-kaca tsakanin jakadun Amurka da Rasha a wajen taron Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, bayan da Amurka ta kira wani taro don tattanawa kan yadda Rasha ke girke dakaru a kan iyakarta da Ukraine.

Jakadiyar Amurka Linda Thomas-Greenfield ta ce aikin girke dakarun na Rasha shi ne irinsa mafi girma da aka taɓa gani a yankin Turai cikin gwamman shekaru.

Takwaranta na Rasha ya zargi Amurka da haifar da ruɗani da kuma yin shisshigi a al’amuran Rasha.

Amurka da Birtaniya sun yi alkawarin ƙara ƙaƙaba wa Rasha takunkumai idan har Rasha ta kutsa Ukraine.

A wajen taron Kwamitin Tsaro na MDD na ranar Litinin, Jakadan Rasha Vasily Nebenzya ya ce babu wata hujja cewa Rasha na da shirin amfani da ƙarfin soji kan Ukraine, kuma MDD ta kasa tabbatar da batun girke dakarun da take yi.

Ya ce Rasha tana yawan girke dakaru a yankinta kuma wannan ba abin da ya shafi Amurka ba ne.

Rasha ta yi ƙoƙarin hana zaman tattanawar kwamitin tsaron a bainar jama’a, amma sai aka rinjaye ta da ƙuri’a 10 inda ita kuma ta tsira da ƙuri’a biyu.

Mr Nebenzya ya ce gwamnatin Biden tana tunzura rikici da tsananta abubuwa.

“Wannan shiga hanci da ƙudundune ne da ake yi wa al’amuran cikin gidanmu, sannan ƙoƙari ne na ɓata mu a idon ƙasashen duniya da kawar da hankalinsu kan ainihin abin da ke faruwa a yankin da kuma dalilan ruɗanin da ake ciki a duniya yanzu,” a cewarsa.

Ms Thomas-Greenfield ta ce Amurka na ci gaba da yin amannar cewa za a samu mafita ta diflomasiyya amma ta yi gargaɗi cewa Amurka za ta ɗauki matakin da ya dace idan har ta kutsa Ukraine, matakan da ba za su yi “daɗi ba.”

Ta ce: “Wannan ne gagarumin… girke dakaru da aka taɓa yi a Turai cikin gwamman shekaru.

“Kuma a yanzu da muke magana, Rasha na aika ƙarin dakaru yankin.”

Fadar Moscow na shirin ƙara yawan dakarunta da ke girke a maƙwabciyarta Belarus, a kan iyakar arewacin Ukraine, zuwa 30,000, in ji ta.

A ranar Litinin da yamma, Amurka ta yi umarnin cewa ma’aikatan gwamnatinta d aiyalansu su bar Belarus, tana mai cewa “akwai damuwa sosai kan girke dakarun da Rasha ke yi.

Sannan ta bayar da irin wannan umarnin ga ma’aikatan gwamnatin Amurka da iyalansu na Ofishin Jakadancin Amurka da ke babban birnin Ukraine wato Kyiv.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button