YAN SANDAN NIGERIA SUNYI NASARAR CHAFKO WANI MUTUN DA,AKE ZARGI BATA GARI CIKIN LAUYOYI.

Rundunar ‘yan-sandan Najeriya tayi awaon gaba da wani mutum da ake zargi lauya ne na bogi da ya dau tsawon lokaci yana waklitar jama’a a kotu a jihar Zamfara.
Rundunar ta gabatar da Chukwuka Jude mai shekara 46 a wani taron manema labarai da kakakinta SP Mohamaed Shehu ya jagoranta a hedikwatarta a Gusau, ranar Litinin din nan 24 ga Janairun, 2022.
Kayayyakin da aka samu a wurin mutumin wadanda rundunar za ta gabatar a matsayin sheda sun hada da, katin shedar aiki na bogi da stamfi da kuma takardun rubuta wasika da ke dauke da sunan kamfaninsa na aikin lauya ; J.N Monyei & Co. Chamber.
A jawabin kakakin ‘yan-sandan ya ce a ranar 18 ga watan nan na Janairu ne 2022, shugaban kungiyar lauyoyi na jihar Zamfara ya gabatar wa da ‘yan sanda kara cewa, a wannan rana an kama wani mutum a cikin Babbar Kotun Shari’a da ke Tudun Wada a Gusau yana gabatar da kansa a matsayin lauya ga wani.
Nan da nan kuma masu bincike na ‘yan-sanda suka shiga aikinsu inda suka nasarar chaf ko mutumin, wanda a yanzu yake hannu yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.
Binciken farko-farko yan una cewa mutumin ya dau tsawon lokaci yana gabatar da kansa a matsayin lauya a kotuna da dama na jihar da suka hada da a kananan hukumomin
Kauran Namoda da Birnin Magaji da Shinkafi kuma Gusau da dai sauran su inda a karshe aka kama shi yana wakiltar wani da ya karbi kudi a wurinsa yana wakiltarsa a matsayin lauya.
Rundunar ta ce mutumin da ake zargi a kokarins ana tsere wa kamu da shari’a ya yi tayin bai wa dan sandan kotu cin hancin naira dubu dari uku, wanda jami’in ya ki karba.